IQNA

'Yan Adawa A Bahrain Sun Bukaci A fito Domin Tabbatarwa Mahukuntan Kasar Rashin Amincewa Da Zaluncinsu

21:25 - May 06, 2012
Lambar Labari: 2319744
Bangaren kasa da kasa, kungiyoyi da jam'iyun adawa a kasar Bahrain sun yi kira ga al'ummar kasar ad su fito kwansu da kwarkwatarsu domin tabbatar wa azzaluman mahukuntan kasar cewa suna nan daram kan bakansu an neman sauyi a cikin harkokin siyasa da mulkin kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-intiqad cewa, kungiyoyi da jam'iyun adawa a kasar Bahrain sun yi kira ga al'ummar kasar ad su fito kwansu da kwarkwatarsu domin tabbatar wa azzaluman mahukuntan kasar cewa suna nan daram kan bakansu an neman sauyi a cikin harkokin siyasa da mulkin kasar wadda ta ke fuskantar babban makirci domin kmurkushe al'ummarta.
Mahukuntan kasar Bahrain sun kama shugaban cibiyar kare hakkin bil adama mai zaman kanta a kasar Nabil Rajab bisa hujjar cewa yana yin kalaman da suke tunzura jama'a domin su yi zanga-zangar bore ga gwamnatin kasar.
Jami'an tsaron kasar ta Bahrain sun kama Nabil Rajab jiya a filin safka da tashin jiragen sama na birnin Manama, a lokacin da yake fitowa daga cikin jirgi bayan dawowarsa daga wani zaman taro na kungiyoyin kare hakkin bil adama da aka gudanar a birnin Beirut na kasar Lebanon, inda suka yi awon gaba da shi ba tare da yi masa wani bayani ba.
A karshen watan Afirilun da ya gataba ma mahukuntan na kasar Bahrain sun kame Nabil Rajab, bisa hujjar shiga zanga-zangar nuna goyon baya mai fafutukar kare hakkokin bil adama Abdulhadi Khawajah, wanda ke yajin cin abinci kuan watanni uku a jere a gidan kurkukun da ake tsare da shi.
1000359

captcha