Kamfanin dillancin labaran inqa ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na OCI cewa, kungiyar kasashen musulmi ta yi kakkausar suka dangane da wulakanta littafan muslunci da aka yi a kasar Mauritaniya da sunan ana neman 'yanci na siyasa wanda a cewar kungiyar babu wata alaka da abin da mutanen suke yi da addini kuma wulakanta muslunci baban laifi ne.
Ko shakka babu samuwar makaman nukiliya, a ko ina ne kuwa a doron duniyan nan, barazana ce ga sulhu da zaman lafiya na kasa da kasa, saboda haka ne manazarta kan tsaro da zaman lafiyar duniya suke cewa bai kamata a ce dokokin NPT na hana yaduwar makaman nukiya su shafi wasu kasashen su kadai alhali wasu kuma suna rike da wadannan muggan makamai ba, wato dai ya kamata a yi adalci a wannan batu mai matukar hadari.
Manazartan sun yi imanin cewa kasa kasashen duniya kaso biyu, ta yanda aka amince wa wasu suka mallakai makaman nukiliya amma wasu kuma a tilasta musu cewa kada su kerasu, ya taimaka wajen gazawa kan magance batun yaduwar makaman, duk kuwa da shudewar shekaru da yawa bayan samar da yarjejeniyar ta hana yaduwar makaman nukiliya.
Sanya siyasa da kuma yin harshen damo a batun hana yaduwar makaman nukiliya shi ne musabbabin da ya kasashe kamar Amurka da Biritaniya da Faransa wadanda suka mallaki dubban kawukan nukiliya suke kokarin hana kasar Iran yin ayyukan nukiliya na zaman lafiya, wadanda kuma take gudanar da su karkashin dokokin kasa da kasa, amma a lokaci guda kuma wadancan kasashe sun rufe idanunsu sun kasa ganin makaman nukiliya da HKI ta mallaka.
1001733