Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: shugabannin kungiyar gwagwarmaya ta musulunci ta neman yantar da Palasdinu Hamas sun bayyana cewa: A yau ne ashirin da watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a wani babban taro da za a gudanar za a tabbatar da matsayi da tarihi mai inganci na Palasdinu da rubuta shi cikin manyan bakake.An nakalto daga majiyar labarai ta CPI cewa; shugabannin kungiyar gwagwarmaya ta Hamas za su gudanar da wani gagaramin taro na nuna tarihin Palsdinu kuma a gurin wannan taro za a samu halartar Isma'il Haniya zaben firaministan yankin Palasdinu da al'ummar Palasdinu suka zaba har ila yau kuma za a samu halartar wakilai da kungiyoyi da hukumomi da mu'assisoshi a yankin Gaza na Palasdinu.
1002734