Bangaren kasa da kasa;mu'assisar da ke kula da jin ra'ayin jama'a dangane da zabe a kasar Faransa ta Opinion Way a safiyar jiya ashirin ga watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ta bayyana cewa; kasha tis'in da uku cikin dari na musulmin da ke a Faransa a zaben shugaban kasa zagaye na biyu suka jefawa Francois Hollande dan takarar jam'iyar Socialiste kuri'arsu da ta kais hi ga lashe zaben inda Nicolas Sarkozy ya sha kayi.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watasa rahoton cewa: mu'assisar da ke kula da jin ra'ayin jama'a dangane da zabe a kasar Faransa ta Opinion Way a safiyar jiya ashirin ga watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ta bayyana cewa; kasha tis'in da uku cikin dari na musulmin da ke a Faransa a zaben shugaban kasa zagaye na biyu suka jefawa Francois Hollande dan takarar jam'iyar Socialiste kuri'arsu da ta kais hi ga lashe zaben inda Nicolas Sarkozy ya sha kayi. An nakalto daga majiyar labarai ta newsring cewa sakamakon ra'ayin jama'a a shafin Internet na kasar Faransa na La Vie ya gudanar da fitar da sakamakonsa ya nuna cewa; a zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar Faransa musulmin kasar sun yi rawar gani wajan taimakawa dan takarar jam'iyar socialiste a kasar Faransa lashe zaben shugabancin kasar ta Faransa da kuma hakan ke nuni da cewa musulmin na kasar faransa na fatar ganin Francois Hollande ya kawo sauyi da canje canje a halayyar da ake nunawa musulmin kasar ta hanyar takura masu a rayuwarsu da kuma nuna masu kahon zuka a fadin kasar ta Faransa.
1003849