IQNA

Zaman Taro Na Nuna Goyon Baya Ga Alummar Bahrain A taron Baje Kolin Littafi

20:46 - May 10, 2012
Lambar Labari: 2322856
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman taro a wajen baje kolin litatfai da ke gudana a birnin Tehran inda aka tattauna kan halin da al'ummar Bahrain suke ciki na zalunci da danniya daga sarakunan kasar da kuma sanin hanyoyin da za a taimaka musu da karfafa musu guiwa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, a yau an gudanar da wani zaman taro a wajen baje kolin litatfai da ke gudana a birnin Tehran inda aka tattauna kan halin da al'ummar Bahrain suke ciki na zalunci da danniya daga sarakunan kasar da kuma sanin hanyoyin da za a taimaka musu da karfafa musu guiwa domin ci gaba da neman hakkokinsu da aka haramta musu.
Bayanin ya ci gaba da cewa a wajen taron an gabatar da jawabai wanda malamai da kuma masana suka yi, domin tabbatar da cewa an kara fito da abin da yake faruwa kan al'ummar Bahrain a fili saboda mutanen duniya kowa ya sani, kasantuwar cewa gwamnatocin kasashen yammacin turai da kafofin yada labaransu suna boye wannan labara, domin da ma su ne suke timaka ma wannan masarauta ta zalunci.
Wannan bayanin ya kara da cewa an gudanar da wani zaman taro a wajen baje kolin litatfai da ke gudana a birnin Tehran inda aka tattauna kan halin da al'ummar Bahrain suke ciki na zalunci da danniya daga sarakunan kasar da kuma sanin hanyoyin da za a taimaka musu da karfafa musu guiwa kan borensu na lumana.
1003972
captcha