Bangaren kasa da kasa, wasu masu fafatuka na kasar Jordan sun yanke kalaman ministan kula da bunkasa harkokin al'adu na kasar Bahrain a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a gaban wani taro a birnin Amman fadar mulkin kasar ta Jordan.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Alalam cewa , wasu masu fafatuka na kasar Jordan sun yanke kalaman ministan kula da bunkasa harkokin al'adu na kasar Bahrain a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a gaban wani taro a birnin Amman fadar mulkin kasar ta Jordan domin nuna rashin amincewa da matakan zalunci da danniya da masarautar kasar take dauka kan fararen hula masu neman hakokinsu na siyasa.
Bayanin ya ci gaba da cewa, tun bayan da mahukuntan kasar Bahrain suka fara daukar matakan yin amfanin da karfin tuwo kan faraen hula da suka hada damaza da mata da kanan yara da dattinaji da suke neman hakkokinsu da aka haramta musu a kasar, kungiyoyin kare hakkin bil adama a kasashen duniya suke ci gaba da mayar da martani.
Masu fafatuka na kasar Jordan sun yanke kalaman ministan kula da bunkasa harkokin al'adu na kasar Bahrain a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a gaban wani taro a birnin Amman fadar mulkin kasar ta Jordan wadda daya ce daga cikin kasashe masu dasawa da masarautar Bahrain.
1005126