IQNA

Duk Da Yana Kana Hanya Amma Ana ci gaba Da Zaluntar Al'ummar Bahrain

17:10 - May 12, 2012
Lambar Labari: 2323989
Bangaren kasa da kasa; juyin juya halin da al'umar Bahrain suka runguma da yin riko das hi yana kan tafarkin gaskiya da daidaito da kuma bai sabawa dokokin na ciki da kuma na kasa da kasa kuma juyi ne na neman kawo sauyi da canji a wannan kasa amma kash ana ci gaba da nunawa al'ummar Bahrain zalunci da danniya ba tare da kungiyoyi na hukumomi na kasa da kasa da sauran kasashen duniya sun ce uffin kan wannan zaluncin.


Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; juyin juya halin da al'umar Bahrain suka runguma da yin riko das hi yana kan tafarkin gaskiya da daidaito da kuma bai sabawa dokokin na ciki da kuma na kasa da kasa kuma juyi ne na neman kawo sauyi da canji a wannan kasa amma kash ana ci gaba da nunawa al'ummar Bahrain zalunci da danniya ba tare da kungiyoyi na hukumomi na kasa da kasa da sauran kasashen duniya sun ce uffin kan wannan zaluncin. A ranar ashirin ga watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya ne bayan kammala taron manema labarai kan ayyukan da suka shafi siyasa da gwagwarmaya a Baharain a dakin taro na fadakarwar musulmi a Musalla gurin da a halin yanzu ake gudanar da kasuwar baje kolin kasa da kasa ta littafai a nan Tehrain karo na ashirin da biyar aka yi nuni da cewa; a yau kowa ya san zalunci da ake nunawa al'ummar Bahrain babu mai kwakwanto kan haka amma kasha babu wani mai cewa uffin ko nuna takaicin kan haka daga cikin hukumomi da kungiyoyi na kasa da kasa ko bukatar kawo sauyi a cikin zalunci da takurawar da ake nunawa wannan al'umma da aka ware da maida ta saniyar ware a fili karara babu mai kwankwanto kan hakan.
1004762
captcha