Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar gwagwamaya ta hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya mayar da hankali kan muhimman batutuwa da suka shafi halin da ake cikin Syria da kuma yankin gabas ta tsakiya baki daya wanda hakan ya mayar da hankulan al'ummomin kaco kaf a kansa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Lebanonfiles cewa, babban sakataren kungiyar gwagwamaya ta hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya mayar da hankali kan muhimman batutuwa da suka shafi halin da ake cikin Syria da kuma yankin gabas ta tsakiya baki daya wanda hakan ya mayar da hankulan al'ummomin kaco kaf a kansa saboda matukar muhimmancinsa a cikin harkokin siyasa da tsaro gami da tattalin arzikin duniya.
Babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya jaddada cewa karfin kungiyar ya lunlunka karfinta na shekarun baya kuma a halin yanzu za su iya kaddamar da hare-hare a cikin birnin Tel aviv matukar dai Haramtacciyar Kasar Isra'ila ta yi wani shishigi a kan Lebanon.
Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana hakan a cikin wani jawabi da ya gabatar a daren jiya da gidajen talabijin da dama suka watsa kai tsaye, dangane da kammala sake gina gidajen da Haramtacciyar kasar Isra'ila ta rusa a kudancin Beirut a lokacin yakin shekara ta 2006, ya ce lokaci ya wuce da yahudawan sahyuniya za su sha lalai a duk lokacin da suka kawo hari kan Lebanon, domin a halin yanzu Hizbullah tana da makaman da za su kai hari a kan muhimman wurare a cikin birnin Tel aviv da ma dukkanin yankunan da ake kira Isra'ila.
Haka nan kuma ya yi kira ga gwamnatocin kasashen musulmi da su safke nauyin da ya rataya kansu wajen taimakon al'ummar Gaza da sake gina musu gidajensu da Haramtacciyar kasar Isra'ila ta rusa a lokacin da ta kaddamar da harin ta'addanci kan al'ummar yankin.
1005079