IQNA

Kawancen Jam'iyyun Kurdawa Bai amince Da Kalaman Batunci Ga Ayatollah sistani Ba

21:14 - May 12, 2012
Lambar Labari: 2324061
Bangaren kasa da kasa, kawance jam'iyyun kurdawa sun nuna rashin amincewa da cin zarafin babban malamin addinin muslunci na kasar Iraki Ayatollah Sayyid Ali Sistani wanda shugaban 'yan sanda birnin Dubai Dahi Khalfan ya yi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Istiqamah cewa, dan majalisar wakilan kasar Iraki Muhsin sa'adun daga kawancen jam'iyyun siyasa na kurdawa ya bayyana cewa, kawance jam'iyyun kurdawa sun nuna rashin amincewa da cin zarafin babban malamin addinin muslunci na kasar Iraki Ayatollah Sayyid Ali Sistani wanda shugaban 'yan sanda birnin Dubai Dahi Khalfan ya yi a cikin kwanakin nan.
Sa'adun ya ce abin mamaki yadda wani mutum kamar Dahi Khalfan har zai iya cin zarafin mutum mai matsayi kamar Sayyid Sistani, wanda shi ba malami ne da mabiya mazhabar shi'a ke komawa gare shi ba ne kawaia akasar, shi malamin dukanin mutanen kasar Iraki, saboda haka ya zama wajibi Khalfan ya nemi gafara a hukumance kan cin zarafin wannan babban malami.
Babban kawance jam'iyyun kurdawa sun nuna rashin amincewa da cin zarafin babban malamin addinin muslunci na kasar Iraki Ayatollah Sayyid Ali Sistani wanda shugaban 'yan sanda birnin Dubai Dahi Khalfan ya yi a 'yan lokutan nan.
1005018
captcha