IQNA

Hadin Kungiyoyin Musulmi A Ghana Sun Soki Lamarin Dan Majaliasar Da Ya Ci Fuskar Musulunci

18:17 - May 15, 2012
Lambar Labari: 2326738
Bangaren siyasa da zamantakewa: hadin kungiyoyin musulmi da yin sulhu na NDC a kasar Ghana sun yi suka da babbar murya kan wani dan majalisar dokoki a kasar da yayi suka da cin fuska kan musulmi da addinin musulunci.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: hadin kungiyoyin musulmi da yin sulhu na NDC a kasar Ghana sun yi suka da babbar murya kan wani dan majalisar dokoki a kasar da yayi suka da cin fuska kan musulmi da addinin musulunci.Alajo Obama dan majalisar dokoki kuma mamba a jam'iyar Demokrat a wannan kasa ana zarginsa da yi wa musulmi zagon kasa da makarkashiya da yin bakaken kalamai masu zabi da bakanta rai kan musulmi da addinin musulunci musamman a daidai wannan kasa da kuma yanayi da ake ciki .
1007773
captcha