IQNA

Za A Kai Gwamnatin Saudiyya Kara A Gaban Kotun Duniya Saboda Laifukan Nuna Wariya

21:20 - May 15, 2012
Lambar Labari: 2326798
Bangaren kasa da kasa, mabiya tafarkin mazhabar iyalan gidan manzon Allah za su kai gwamnatin Saudiyya kara a gaban kotun manyan laifuka ta duniya saboda matakan rashin imani da nuna wariya ga ‘yan asalin kasar da take nunawa saboda suna bin tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Muhit cewa, mabiya tafarkin mazhabar iyalan gidan manzon Allah za su kai gwamnatin Saudiyya kara a gaban kotun manyan laifuka ta duniya saboda matakan rashin imani da nuna wariya ga ‘yan asalin kasar da take nunawa saboda suna bin tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka tare da yi musu kisan gilla saboda sun ce suna neman hakkokinsu da aka haramta musu.
A nata bangare kungiyar kare hakkin bil'adama ta kasa da kasa "Amnesty International "ta bukaci a gudanar da bincike akan kisan da jami'an tsaro su ka yi wa wani mai zanga-zanga a gabacin saudiyya, a wani bayani da kungiyar ta kare hakkin bil'adama ta fitar ta bukaci a yi bincike mai zaman kanshi akan kisan da aka yi wa Isam Muhammad Abu Abdullah a lokacin da ya ke cikin zanga-zanga a garin Awamiyyah da ke gabacin Saudiyya da ma wasu garuruwan da ke yankin.
Wannan zanga-zangar ta ranar alhamis din da ta gabata an yi ta ne domin kira da a saki fursunonin siyasa da ake tsare da su da kuma kawo karshen wariyar da ake yi wa 'yan shi'a a yankin, a cikin watannin bayan nan dai jami'an tsaron Saudiyya sun rika bude wuta akan masu zanga-zangar lumana da su ke son a samar sa sauye-sauye na siyasa a cikin kasar tare da kawo karsehn mulkin kama karya.
1007393


captcha