Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Press TV cewa, a daidai lokacin da zabuka ke ci gaba da karatowa akasar Amurka kyamar musulmi a kasar na ci gaba da karuwa musamman a bangaren wadanda bas u boye tsananin kiyayyarsu da addinin muslunci da musulmi a kasar wadanda a lokutan baya suka kone kr'ani da ma wasu ayyuka na batunci ga muslunci.
A nasa bangaren a wata hira da yayi da kafafen yada labaran kasar Rasha, wanda a cikinsu har da kamfanin dillancin labarai na Ria Novosti, Hamid Karzai, shugaban kasar Afghanistan, ya shaida cewa shekaru 10 na nato a kasar ta Afghanistan ba su tabbatar da tsaro ko samar da zaman lafiya a kasar ba. Rishin tsaron da ake fama da shi a kasar ba Afghanistan kadai matsalar ta shafa ba, amma matsala ce da ta shafi duniya baki daya don haka ya zama dole a taru a magance ta, inji Mista Karzai. Ko a cikin sabbin ayukan kungiyoyin ta'addanci a cikin kasar ta Afghanistan, a ranar lahadi da ta gabata sun kashe wani mamba na majalisar koli ta zaman lafiya, mai suna Arsalan Rahmani, a cikin garin Kaboul.
Magabatan kasar ta Afghanistan, na dora laifin nuna halin ko in kula da kasashen yammaci ke nunawa a game da bukatar horon jami'an tsaron kasar da basu kayan aikin da ya dace, alhalin hakan na tafe kafada da kafada da tsarin na hannanta harakar tsaron a hannun jami'an tsaron kasar. A daya waje bayan kasawar da dakarun kasashen ketare wajen dakatar ko dakile ayukan kungiyoyin yan ta'ada a cikin kasar da kuma kawo karshen tashin hankalin da ake fuskanta a kasar, wanda shine wani bangare na rishin tsaron da kasar ta ke fama da shi, wannan ko duk sun biyo bayan dabi'u marar kyau da dakarun Amurka da na nato ke nuna da cewarsu wai suna yaki ne da ta'adanci, matakai ko taketaken da har yanzu ba wani sakamako na gari da aka samu daga ita illa kisan fararen fula da aka karkashe, tare da ruguza muhalinsu.
1008527