Bangaren kasa da kasa, shugaban cibiyar alkur’ani mai tsarki ta kungiyar magoya bayan Sadr a kasar Iraki ya bayyana cewa ya zuwa dai kimanin kasashe 26 ne daga cikin kasashen musulmi dan alarabawa suka tabbatar da cewa za su hakarci gasar karatun kur’ani mai tsarki daharda da za a gdanar a kasar Iraki wanda wannan cibiya za ta dauki nauyin shirya da gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin wata zantawa da ta hada shi da sheikh Mazin Sa’idi shugaban cibiyar alkur’ani mai tsarki ta kungiyar magoya bayan Sadr a kasar Iraki ya bayyana cewa ya zuwa dai kimanin kasashe 26 ne daga cikin kasashen musulmi dan alarabawa suka tabbatar da cewa za su hakarci gasar karatun kur’ani mai tsarki daharda da za a gdanar a kasar Iraki wanda wannan cibiya za ta dauki nauyin shirya da gudanarwa acikin makonni masu zuwa.
Wani labarin kuma yana cewa yanzu haka an fara gudanar da wani taron bayar da horo ga sojojin kasar Burnei kan karatun kur’ani mai tsarki da kuma harda ta yadda hakan zai ba su damar sanin hanyoyon karfafa karatu da harda littafin mai tsarki kamar dai yadda aka saba yi a kasar.
Burnei na daga cikin kasashen musulmi da suke bayar da matykar muhimamnci ga lamurra da suka danganci a ddinin muslunci a cikin dukaknin harkokin kasar, da suka hada da na gwamnati na jama’a daidauiku, da hakan ya hada lamurran soji na tsaro a kasar ta Burnei.
Gudanar da wani taron bayar da horo ga sojojin kasar Burnei kan karatun kur’ani mai tsarki da kuma harda ta yadda hakan zai ba su damar sanin hanyoyon karfafa karatu da harda littafin mai tsarki yana da matukar amfani ga rundunar soji ta kasar musulmi, domin ko ba komai hakan zai ba su damar yin aikinsu bisa koyarwar addininsu.
1009538