Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar gwagwarmayar msulunci ta hizbullah Sayyid Hassan nasrullah ya gudanar da wata tattaunawa tare da jagoran kungiyar Jabha Ahmad Jiril kan muhimman batutuwa da suka danganci yanayin da ake cikin yanzu haka a yankin gabas ta tsakiya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin Almanar ta kasar Lebanon cewa, babban sakataren kungiyar gwagwarmayar msulunci ta hizbullah Sayyid Hassan nasrullah ya gudanar da wata tattaunawa tare da jagoran kungiyar Jabha Ahmad Jiril kan muhimman batutuwa da suka danganci yanayin da ake cikin yanzu haka a yankin gabas ta tsakiya da ma wasu batutuwa da suka danganci bangarorin biyu.
Sakataren na kungiyar gwagwarmayar musulunci a kasar Lebanan Sayyid Hassan nasrullah ya jadadda goyon bayansa ga jagoran juyin juya halin muslunci da kuma shugaban jamhuriyar musulunci ta Iran kan gagarumar gudunmawar da suke bayarwa adukaknin bangarori na ci gaba n al’ummar musulmi.
Sayyid Nasrullah a halin yanzu dai shi ne jagora na farko da ya gasa wa haramtacciyar kasar Isra’ila aya a hannunta a lokacin da ta kaddamar da yaki kan al’ummar kasar Lebanon a cikin shekara ta dubu biyu da shida, inda dakarun hizbullah suka fatattaki sojojin yahudawan sahyuniya, kuma su fice daga kasar babu shiri a cikin kaskanci.
1009271