IQNA

Wani Dan Majalisa A Kazakhstan Ya Yi Kira Da Hana Watsuwar Akidar Wahabiyanci

21:44 - May 17, 2012
Lambar Labari: 2328094
Bangaren siyasa da zamantakewa, wani dan majalisar dokokin kasar Kazakhstan ya yi kira da a dauki kwararan matakai na hana yaduwar akidar wahabiyanci a kasar saboda bababn hadarin da wannan akida take dauke da shi a cikin al’ummar musulmi da ma sauran adam baki daya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Kazakhstan cewa wani dan majalisar dokokin kasar ya yi kira da a dauki kwararan matakai na hana yaduwar akidar wahabiyanci a kasar saboda bababn hadarin da wannan akida take dauke da shi a cikin al’ummar musulmi da ma sauran adam baki daya, musamman idan aka yi la’akjari da cewa duik wani ta’addanci da ake fama da shi a duniya da ake yi amfani da sunan muslunci ya samo asali ne daga akidar wahabiyanci.
Da dama daga cikin masana da malam,an addinin muslunci sun amannar cewa, haramtacciyar kasar Isra’ila ce take amfana da salon siyasar dabbanci da wawanci da wuce gona da iri ta mabiya tafarkin salafiyya da suke cikin gwamnatin kasar Masar a halin yanzu inda suke bata sunan muslunci da bakanta fuskarsa da siyasara mai tsarki a idon duniya kamar yadda kowa ya gani a cikin ‘yan watanni da suka yi mulki.
A kasar Jamus kuwa ministan harkokin cikin gidan kasar ne ya yi kakkausar suka kan mabiya tafarkin salafiyya dangane da abubuwan da suke yi a kasdar na wuce gona da iri da sunan cewa suna bin tafarkin addinin mulsunci ne da kuma rarraba kur’anai a tsakanin al’ummar kasar ta Jamus.
A bangare guda kuma ana shirin gudanar da wani shiri na musamman dangane da bayar da horo ga limaman masallatai na kasar Jamus, wanda jami’ar Snaburg ta kasar za ta dauki nauyin aiwatar da shi tare da hadin gwai da cibiyoyin mabiya addinin muslunci na kasar baki daya, wanda kuma ake ganin zai amfani matuka.
Bayanin ya ci gaba da cewa, kasar Jamus na da musulmi da yawansu ya haura miliyan hudu a fadin kasar, saboda haka wannan jami’a ta dauki nauyin bayar da karatu kan muhimman abubuwan da ya kamata masu jagorancin masallatai su koya kafin fara limanci, wanda kuma malaman addinin muslunci ne za su koyar da su a jami’a bisa tsari na karatun digiri.
Gudanar da wani shiri na musamman dangane da bayar da horo ga limaman masallatai na kasar Jamus, wanda jami’ar Snaburg ta kasar za ta dauki nauyin aiwatar da shi tare da hadin gwai da cibiyoyin mabiya addinin muslunci, hakan na da matukar alfanu ga musulmi.
1008940


captcha