Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Bayan kammala zaben shugabancin kasa a tsakanin yan takarar da ke fafatawa neman shugabancin wannan kasa an bayyana cewa yan takara masu ra'ayi na addinin musulunci ne ke kan gaba dag a cikin kuri'un da aka kada way an takarar a ketare da hakan ke nuni da yadda al'ummar kasar ke fatar ganin masu ra'ayin addini da kuma addinin musulunci da koyarwa ta addinin musulunci yayi rawar gani a wannan kasa da yawancin al'ummar kasar musulmi ne. Duk da cewa 'yan kwanaki suka rage kafin gudanar da zaben shugaban kasar Masar na farko tun bayan kifar da gwamnatin kama karya ta Hosni Mubarak, to amma bangarori daban-daban a kasar suna ta nuna damuwarsu dangane da abin da suka kira kokarin da sojoji masu mulki a kasar suke yi na tsoma baki cikin harkar zaben da nufin magudi. Masu wannan tunanin dai suna ishara ne da irin kokarin da majalisar koli ta sojin tare da hadin bakin masu adawa da juyin juya halin da aka yi a kasar Masar din na ciki da wajen kasar suka yi wajen ganin sun karkatar da manufar juyin da kuma ganin cewa juyin bai kai ga manufar da ya sa a gaba ba.
Masu wannan ra'ayin dai suna bayyana cewar tun da farko dai sojojin wadanda gyauron tsohuwar gwamnatin Mubarak din ne da sauran masu goya musu baya sun fara ne da kokarin haifar da fitina tsakanin mutanen Masar din da kuma amfani da karfi wajen kawo karshen irin zanga-zangar nuna rashin amincewa da mulkinsu da kuma kokari wajen ganin ba a gudanar da zaben 'yan majalisar kasar da aka gudanar a baya ba. To sai dai kuma tsayin dakan al'umma ya tilasta musu gudanar da wannan zaben inda masu kishin Musulunci suka lashe zaben wanda hakan bai yi dadi wa masu adawa da juyin na ciki da waje ba. A saboda haka ne suka koma ga wata siyasar ta daban duk dai da nufin mamaye juyin da juya shi zuwa ga bangaren da suke so. Daya daga cikin hanyoyin da za su iya cimma hakan shi ne tsoma bakinsu cikin harkar zaben shugaban kasar da za a gudanar ta hanyar wasu hanyoyi da dabaru daban-daban wanda mafi muhimmancin cikinsa shi ne shigo da Umar Sulaiman tsohon shugaban cibiyar leken asirin Masar din a lokacin Hosni Mubarak a matsayin dan takarar zaben da kuma yin watsi da takarar tasa daga baya don haka ya share musu fagen yin watsi da takarar wasu daga cikin fitattun 'yan takarar da za su tsaya wadanda kuma za su iya zama musu kafar ungulu mafi muhimmancinsu shi ne asalin dan takarar jam'iyyar 'yan Ikhwan al-Muslimin wato Khairat Shatir.
To sai dai kuma sakamakon zaben shugaban kasar da aka fara gudanarwa a wajen kasar wanda aka fitar da shi shekaran jiya juma'a na nuni da cewa sojojin da masu goya musu bayan ba su yi nasara ba wajen kawar da masu kishin Musuluncin daga fage sakamakon irin nasarar da suka samu a zaben, kamar yadda kuma kididdigar jin ra'ayin jama'a ma na nuni da cewa 'yan takara masu kishin addinin suna nan daram a fagen zaben shugaban kasar.
Irin wadannan abubuwa da majalisar koli ta soji mai mulkin ta dinga gudanarwa ne ya sanya al'ummar Masar din a yankuna daban-daban nuna damuwarsu ainun da kan yiyuwar gudanar da magudin a lokacin zaben. Hakan ne ma ya sanya wasu 'yan majalisar kasar gabatar da wani kuduri a majalisar don tattaunawa irin barazanar da zaben shugaban kasar yake fuskanta da kokarin da ake yi na ganin 'yan takara masu kishin Musulunci da kuma adawa da bakar siyasar kasashen yammaci da HKI ba su yi nasara a zaben ba.
Wani lamarin kuma da yake ci gaba da janyo hankulan Misirawan shi ne irin yadda wasu kasashen larabawa suka shigo da karfinsu da dukiyarsu wajen goyon bayan wasu 'yan takaran irin su tsohon firayi ministan kasar lokacin Mubarak Ahmad Shafiq da tsohon babban sakataren kungiyar kasashen larabawa Amr Musa wadanda suke ganin idan har suka ci zabe za su ci gaba da lamunce musu bakaken manufofinsu a kasar Masar din kamar yadda Hosni Mubarak ya kasance yana yi.
To sai dai kuma daga dukkan alamu al'ummar kasar Masar sun kuduri aniyar kare kuri'unsu kamar yadda suka yi a lokacin da aka gudanar da zaben 'yan majalisar kasar sannan kuma ba za su taba amincewa da kokarin da ake yi na mayar musu da hannun agogo baya ba bayan dukkanin irin sadaukarwar da suka yi wajen fatattakar lalatacciyar gwamnatin Hosni Mubarak 'yar amshin shatan Amurka da HKI ba.
1011140