IQNA

Amirin Kasar Koweiti Ya Yi Watsi Da Maida Dokokin Kasar Irin Na musulunci

16:36 - May 20, 2012
Lambar Labari: 2330088
Bangaren kasa da kasa; Amirin kasar koweiti ya fito fili ya yi watsi da nuna adawarsa da shawarar da aka bayar na aiki da shari'ar musulunci a kasar ma'ana a canja kundin tsarin mulkin kasar da ke aiki a halin yanzu a kasar da maiye gurbinsa da shari'ar musulunci.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Amirin kasar koweiti ya fito fili ya yi watsi da nuna adawarsa da shawarar da aka bayar na aiki da shari'ar musulunci a kasar ma'ana a canja kundin tsarin mulkin kasar da ke aiki a halin yanzu a kasar da maiye gurbinsa da shari'ar musulunci.Kaso talatin cikin hamsin nay an majalisar dokoki a kasar Koweiti sun bukaci sheikh Sabah Jabir Alsabah amirin kasar Koweiti kan ya amince da yin wasu canje canje da sauye sauye a cikin kundin tsarin mulkin kasar da hakan zai kai ga tabbatar da shari'ar musulunci a wanna kasar amma sai nan take bad a wata wata bay a bayyana adawarsa a fili kan wannan shawara.Muhammad Aldalal dan majalisar dokoki a wannan kasa ta Koweiti kuma masanin hakkokin dan adam ya bayyana cewa: wannan shawara ta samo asali ne daga komitin adalci irin na musulunci tare da sanya hannu na amincewa da shawarar daga wakilan majalisar kasar su talatin da daya.

1011125

captcha