Bangaren kasa da kasa, Tsawon shekaru kasashen yammacin turai musamman kasar Amurka tana kallon gwamnatin Saudiyya a matsayin mai kare manufofinta a yankin gabas ta sakiya tare da kawo cikas ga duk wani yunkuri daga kasashen larabawa ko na musulmi da ke yankin da suke da wata manufa ta taimakon palastinawa da ‘yantar da su daga danniyar haramtacciyar kasar Isra’ila.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, tun tsawon shekaru kasashen yammacin turai musamman kasar Amurka tana kallon gwamnatin Saudiyya a matsayin mai kare manufofinta a yankin gabas ta sakiya tare da kawo cikas ga duk wani yunkuri daga kasashen larabawa ko na musulmi da ke yankin da suke da wata manufa ta taimakon palastinawa da ‘yantar da su daga danniyar haramtacciyar kasar Isra’ila musamman mamasu ra’ayin kishin larabci da kuma irin su Syria, da kuma masu kishin islama irin jamhuriyar musulunci.
Lokacin da malaman addinin muslunci na hakika suke ci gaba da hankoron ganin an samu fahimtar juna tsakanin dukaknin al’ummomin duniya tare da zaman lafiya wasu daga cikin masu kiran kansu malaman addini a kasar Sudiyya suna fitar da fatawoyin halascin kai hari kan saura mabiya addinai kamar majamioin mabiya addinin kirista.
A cikin wanmnan makon ne wani mutum da ake kira mai bayar da fatawa na gwamnatin Saudiyya Abdulaziz Bin Abdullah Al-sheikh, ya fitar da wata fatawa daga mahangarsa ta akidar wahabiyanci da ke kafirta musulmi kansu wadanda ba su bin wannan tafarki na wahabiyanci, inda ya halasta kaddamar da kai hare-hare kan wuraren ibadar mabiya addinin kirista.
Masana da dama suka ganin a lokacin malaman addinin muslunci na hakika suke ci gaba da hankoron ganin an samu fahimtar juna tsakanin dukaknin al’ummomin duniya tare da zaman lafiya wasu daga cikin masu kiran kansu malaman addini a kasar Sudiyya suna fitar da fatawoyin halascin kai hari kan saura mutane da ba musulmi ba.
1012156