IQNA

Wahabiyawa Na Barazanar Rusa Hubbaren Sayyida Rukayya A Kasar Syria

17:37 - May 21, 2012
Lambar Labari: 2330980
Bangaren kasa da kasa, mabiya tafarkin wahabiyanci da kafirta sauran al’ummar musulmi suna barazanar kaddamar da harin ta’addanci kan hubbaren Sayyida Rukayya (SA) dake birnin Damascus fadar mulkin kasar kamar dai yadda wata majiya mai tushe akasar ta tabbatar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na nun cewa, ‘yan ta’adda mabiya tafarkin wahabiyanci da kafirta sauran al’ummar musulmi suna barazanar kaddamar da harin ta’addanci kan hubbaren Sayyida Rukayya (SA) dake birnin Damascus fadar mulkin kasar kamar dai yadda wata majiya mai tushe a kasar ta sheda da hakan.
A nasa bangaren mai bayar da fatawa a kasar Syria sheikh Badruddin Hassun ya bayyana cewa, a farkawar mabiya a ddinin muslunci a sassa na kasashen musulmi mabiyar mazhabobin shi’a da sunna sun farka a karkashin kalmar Allahu Akbar ba tare da nuna wani banbanci ko ta’assubanci a tsakaninsu ba kamar dai yadda muke shedawa a halin yanzu a cikin kasashen larabawa.

A jawabin Muftin kasar Siriya Sheikh Badruddeen Hasun ya fara ne da jinjinawa shugaban kasar Iran Dr Mahmud Ahmadin Najad da cewa: Hakika babban abin alfahari ne gare ni ganin shugaban kasar Iran ya fara gabatar da jawabinsa a gaban mumbarin Majalisar Dinkin Duniya da salati ga manzon Allah da iyalan gidansa, kuma yana magana da duniya da kalmar addinin Musulunci wanda da ita ce Allah ya daukaka mu.

Sheikh Hasun ya kuma bayyana cewa: Hakika mu al'ummar musulmi al'umma guda ne kafin kasancewarmu 'yan shi'a ko 'yan sunna, kuma duk wata mahangarmu tana bayan mahangar annabinmu ne da na jikansa Ja'afar Sadiq, don haka wannan shi ne tushen hadin kai.

Manufar gudanar da zaman taron kasa da kasa kan hadin kai tsakanin mazhabobin Musulunci ita ce shimfida matakan samar da hadin kai da taimakekkeniya tsakanin al'ummar musulmi da irin rawar da malamai zasu taka a fagen samar da kusancin ra'ayi a fannonin ilimi musamman a bangaren ilimin fikihu, usulu, akida, tafsirin alkur'ani da sauransu, kamar yadda zaman taron ke tattauna al'amuran kasashen musulmi da matsalolin da ke addabar musulmi da neman hanyar warware su.

1012115



captcha