IQNA

Fatawar Jagora Babban dalili Ne Ke Tabbatar Da Sahihanci Shirin Nukiliyar Iran Na Zaman lafiya

13:00 - May 22, 2012
Lambar Labari: 2331587
Bnagaren kasa da kasa, fatawar da jagoran juyin juya halin muslunci a Iran ya bayar dangane da haramcin kera ko mallakar makaman nukiliya babban dalili ne da ke tabbatar da cewa shirin jamhuriyar muslunci ta Iran na zaman lafiya ban a kera makaman kare dangi ba.

Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a zantawar da ta hada shi da daya daga cikin malaman addii yankin kudancin kasar Lebanon Sheikh Mustafa Muhammad Al-misri Al-amuli y abayyana cewa fatawar da jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayar dangane da haramcin kera ko mallakar makaman nukiliya babban dalili ne da ke tabbatar da cewa shirin jamhuriyar muslunci ta Iran na zaman lafiya ban a kera makaman kare dangi ba kamar yadda kasashen yammacin turai suke ta hankoron bayyanawa.
Y ace tsarin tsarin jamhuriyar muslunci ta Iran ya sha banban da dukkanin tsaruka na kasashen duniya, domin kuwa Iran tsainta na mulki da siyasa da gudanarwa ya ginu ne kan addini da maanga ta addini wadda malamai ke fayyacewa, saboda haka abin da ya jagora ya fitar da fatawar haramcinsa ya haramta a cikin tsarin jamhuriyar muslunci ta Iran, wanda kuma makiya bas u fahimci hakan ba.
Fatawar da jagoran juyin juya halin muslunci a Iran ya bayar dangane da haramcin kera ko mallakar makaman nukiliya babban dalili ne da ke tabbatar da cewa shirin jamhuriyar muslunci ta Iran na zaman lafiya ban a kera makaman nukiliya ba.
1013130

captcha