IQNA

Kyamar Musulmi Na Karuwa A takanin Al'ummar Kasar Holland

20:13 - May 22, 2012
Lambar Labari: 2331933
Bangaren kasa da kasa, rahotanni suna tabbatar da cewa kyamar musulmi na karuwa fiye da kowane lokaci a kasar Hollad sakamon ayyukan farfagandar karya da wasu amsu adawa da mmusulunci suke yi a kasar wanda kuma hakan yak an yi tasiri a cikin kwakwalen wasu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakato daga shafin sadarwa na yanar gizo na press tv cewa, rahotanni suna tabbatar da cewa kyamar musulmi na karuwa fiye da kowane lokaci a kasar Hollad sakamon ayyukan farfagandar karya da wasu amsu adawa da mmusulunci suke yi a kasar wanda kuma hakan yak an yi tasiri a cikin kwakwalen wasu daga cikin mutanen kasar.
A wani labara kuma kasar Iran ta jaddada matsayinta na ci gaba da taka gagarumar rawa domin ganin cewa an kwance wa duniya damarar nukiliya da kuma sauran makamai masu guba da suka cika duniyar sannan kuma suke yi wa zaman lafiya barazana.
Shugaban tawagar masu tattaunawa kan shirin nukiliyar ta Iran Sa'id Jalili ne ya jaddada hakan a lokacin da yake ganawa da shugaban Hukumar Sanya Ido kan Ayyukan Nukiliya ta Duniya Yukiya Amano wanda yake gudanar da ziyarar aiki a nan Iran a yau linitin, inda ya ce akwai bukatar wannan hukuma ta taka rawar da ta dace da ita da kuma gudanar da ayyukanta a cikin 'yan ci kamar dai yadda dokoki suka shata mata.
Shi dai Yukiya Amano yana gudanar da ziyarar aiki a kasar ta Iran ne a daidai lokacin da ake shiri shiga zagaye na gaba na tattaunawa tsakanin Iran da kuma gungun kasashen nan 5 masu kujerun dindindin a Majalisar Dinkin Duniya gami da kasar Jamus, taron da zai gudana a ranar 23 ga wannan wata na Mayu. Amano dai yana tare da rakiyar manyan jami'an hukumarsa da suka hada da babban sipeton hukumar Herman Nackaerts da mataimakinsa mai suna Rafael Mariano Grossi.
1013079

captcha