IQNA

Za A Gudanar Da Zaman Taron Na Hadin Gwiwa Tsakanin Kungiyar Kasashen Musulmi Da Tarayyar Turai

20:45 - May 22, 2012
Lambar Labari: 2331943
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da zaman tattaunawa tsakanin kungiyar kasashen musulmi da kuma kungiyar tarrayar turai wanda zai gudana a birnin Brussel na kasar Belgium da nufin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci alaka tsakaninsu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Riyad cewa, za a gudanar da zaman tattaunawa tsakanin kungiyar kasashen musulmi da kuma kungiyar tarrayar turai wanda zai gudana a birnin Brussel na kasar Belgium da nufin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci alaka tsakanin kasashensu da kuma al'ummominsu.
Taron koli na kasashen Kungiyar NATO da ke gudana a birnin Chicago na kasar Amurka, ya fitar da sanarwar da ke jaddada matsayin kasashen na janye sojojinsu daga Afghanistan a karshen shekara ta 2014, sannan kuma da ci gaba da tallafa wa kasar domin hana wa 'yan Taliban sake dawowa a kan karagar mulki.
Shuwagabanni da kuma wakilan gwamnatocin kasashen kungiyar fiye da 50 da ke halartar wannan taro, a rana ta biyu sun yi kokarin nuna wa duniya cewa kawunansu a hade suke wajen ci gaba da yakar kungiyar ta Taliban da kuma Alka'ida a kasar ta Afghanistan, to sai dai a fili take cewa ba dukkanin kasashen ne ke da niyyar ci gaba da barin sojansu a kasar ta Afghanistan har zuwa karshen shekara ta 2014 ba.
Daga cikin kasashe fiye 50 mambobin kungiyar ta Nato, 28 ne kawai suka amince da barin sojojinsu a kasar har zuwa lokacin da jagorar wannan yaki wato Amurka za ta fice daga kasar baki daya wato karshen 2014, yayin da sauran kasashen cikinsu kuwa har da Faransa mai sojoji 3,500 a fagen dagar a bayyana shirinta na janyewa kafin kashen wannan shekara da muke ciki.
1013270


captcha