IQNA

Sayyid Nasrullah Ya Yi Kakkausar Suka Kan Garkuwa Da Wasu ‘Yan Lebanon A Syria

12:03 - May 24, 2012
Lambar Labari: 2333024
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah a kasar Lebanon ya yi kakakusar suka kan sace wasu masu ziyarar addini ‘yan asalain kasar Lebanon da wasu ‘yan ta’adda suka yi a kasar Syria a lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida a garin Halab.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin di Almanar cewa, Sayyid Hassan nasrullah babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah a kasar Lebanon ya yi kakakusar suka kan sace wasu masu ziyarar addini ‘yan asalain kasar Lebanon da wasu ‘yan ta’adda suka yi a kasar Syria a lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida a garin Halab dake cikin kasar ta Syria, tare da yin kira ga iyalan mutanen da ake yin garkuwa da su da su yi hakuri su kwantar da hankulansu.
Sojojin Syria sun kutsa wani wuri da ake tsammanin cewa, masu makamai a garin Halab sun yi garkuwa da mutanen Lebanon da su ke kan hanyarsu ta komawa gida, a jiya da rana ne dai wasu mutane mutane da ke dauke da makamai a garin Halab na Syria su ka tsaida motar safa da ta ke dauke da mutanen Lebanon da su ke kan hanyarsu ta komawa gida bayan sun kai ziyara Iran, tare da yin awon gaba da dukkanin mazajen 11 da su ke cikinta.
Watsuwar labarin a kasar Lebanon ya haddasa fusatar mutane da fito kan tituna da kuma kona tayoyi da datse manyan hanyoyi a garurwa daban-daban da su ka hada da Beirut, babban magatakardar kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah ya yi gajeren jawabi ta hanayr telbijin din al-manar da a cikin ya bukaci mutane da su bude manyon hanyoyi tare da tabbatar musu da cewa, suna gudanar da tuntubar duk wadanda su ka dace domin kawo karshen matsalar, tuni dai rayuwa ta sake komawa daidai a cikin birnin na Beirut bayan jawabin Sayyid Hassan Nasarallah.
1014732



captcha