Bangaren kasa da kasa, gugn matasa na watan Fabrairu a kasar Bahrain ya bayyana cewa ya gudanar da gagarumar zanga-zanga ne a kasar domin nuna rashin amincewa da taimakon da Amuka take baiwa sarakunan kasar domin ci gaba da murkushe fararen hula masu zanga-zangar lumana domin neman sauyi na siyasa da kuma sayar da makamai ga gwamnatin kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tawafuq cewa, gugn matasa na watan Fabrairu a kasar Bahrain ya bayyana cewa ya gudanar da gagarumar zanga-zanga ne a kasar domin nuna rashin amincewa da taimakon da Amuka take baiwa sarakunan kasar domin ci gaba da murkushe fararen hula masu zanga-zangar lumana domin neman sauyi na siyasa da kuma sayar da makamai ga gwamnatin kasar domin yin amfani das u kan fararen hula.
A ani labarin kuma Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta yi suka da kakkausar murya akan yadda ake murkushe 'yan hammayya a cikin kasar Saudiyya a cikin rohotonta na shekara-shekara kungiyar ta Amnesty ta ce: "Yunkurin da al'ummar Saudiyya din su ke yi wanda ya samo asali ne daga abinda ya ke faruwa a cikin sauran kasashen yankin, ya fuskanci murkushewa mai tsanani daga mahukuntan kasar."
Kungiyar ta Amnesty International ta ci gaba da cewa: " Mahukuntan na Saudiyya sun kame mutane masu yawan gaske mafi yawancinsu masu kare hakkin bil'adama wadanda su ka rika nuna kin amincewarsu a shekarar da ta gabata ta 2011."
Kungiyar kare hakkin bil'adaman ta ci gaba da cewa: Da akwai dubban mutane a cikin gidajen kurkukun saudiyya kuma suna fuskantar azabtarwa da kuma cin zarafi."
1016104