Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalato daga shafin sadarwa na yanar gizo an gudanar da wani zaman taro a kasar Pakistan na bincike kan harkokin ilimi na addinin muslunci tare da halartar masana daga sassan na kasar da suka hada da malaman addini da kuma na jami'a wadanda suka gabatar da laccoci da kuma kasidu.
Wani rahoton na daban kuma yana cewa kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ta yi Allah wadai kan take hakkin dan Adama da ake yi a kasar Maroko, a rahoton da kungiyar ta Amnesty International ta fitar a yau juma'a ta yi kakkausar suka kan irin yadda ake take hakkin dan -Adama da cin zarafinsa a kasar Maroko da suka hada hana tofa albarkacin baki, azabtarwa a gidajen kurkuku, murkushe masu zanga zangar lumana da kame 'yan jarida.
Rahoton ya kuma kara da cewar a kasar Maroko ana kame 'yan jarida da masu kafofin watsa labarai tare da tsare su a gidajen kurkuku saboda sun yi suka kan mahukunta ko watsa rahoto dangane da yadda ake tafiyar da harkar siyasa a kasar.
Gudanar da wani zaman taro a kasar Pakistan na bincike kan harkokin ilimi na addinin muslunci tare da halartar masana daga sassan na kasar da suka hada da malaman addini da kuma na jami'a, hakan yana da baabn tasirin wajen zaburar da masu nazari kan harkokin bincike na ilimi.
1015946