IQNA

An Yi Zanga-zangar Nuna Rashin Amincewa Da Keta Alfarmar Kur’ani A Afghanistan

15:21 - May 27, 2012
Lambar Labari: 2335258
Bangaren kasa da kasa, dubban mutanen sun gudanar da zanga-zangar kin amincewa da keta alfarmar kur’ani mai tsarki da sojojin mamayar Amurka suka yi a yankin maidan wardak na kasar wanda suka yi ta rera taken la’anta g Amurka da ‘yan korenta da suke cin mutuncin musulmi da addinin muslunci domin tsokana.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa dubban mutanen sun gudanar da zanga-zangar kin amincewa da keta alfarmar kur’ani mai tsarki da sojojin mamayar Amurka suka yi a yankin maidan wardak na kasar wanda suka yi ta rera taken la’anta g Amurka da ‘yan korenta da suke cin mutuncin musulmi da addinin muslunci domin tsokana ga musulmi.
Majalisar mabiya addinin muslunci a kasar Faransa za ta shigar da kara kan mutanen da suek nuna matuar adawa da addinin muslunci a kasar faransa saboda abin da suke yi na kokarin haddasa rikici da rashin fahimtar juna tsakanin mabiya addinin musulunci da sauran mabiya addainai da suke zaune a kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa kasar Faransa na daga cikin kasashen nahiyar turai da suka fi yawan musulmi, ta yadda adadinsu ya zama su ne na biyu ta fuskacin yawa a kasar bayan mabiya addinin kiristanci, amma kuma duk da haka har yanzu gwamnatin kasar ba ta amince da addinin musulunci a hkumance ba amatsayin daya daga cikin addinain kasar, duk kuwea da cewa ta amince da addinin yahudanci.
Shigar da kara kan mutanen da suke nuna matuar adawa da addinin muslunci a kasar faransa saboda abin da suke yi na kokarin haddasa rikici da rashin fahimtar juna tsakanin mabiya addinin musulunci da sauran mabiya addainai, yin hakan zai zama tamkar wani hannunka mai sanda ga sauran masu irin wannan akida asauran kasashen turai.
1017133




captcha