IQNA

Kungiyar Afuwa Ta Duniya Ta Yi Kakkausar Suka Kan Tauyen Hakkokin ‘Yan Adam A Saudiyya

21:52 - May 27, 2012
Lambar Labari: 2335460
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kare hakkin bil adama ta duniya Amnesty international ta yi kakkausar suka kan masarautar kasar Saudiyya ta gidan sarautar Al-saud da suke mulki a kasar kan danne hakkokin bil adama da suke yi a kasar musamman mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah marassa rinjaye.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alalam cewa, kungiyar kare hakkin bil adama ta duniya Amnesty international ta yi kakkausar suka kan masarautar kasar Saudiyya ta gidan sarautar Al-saud da suke mulki a kasar kan danne hakkokin bil adama da suke yi a kasar musamman mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah marassa rinjaye wadanda aka mayar da su saniyar ware a cikin harkokin kasar.
A wani batun kuma masana da dama sun amannar cewa ficewar dakarunnato daga kasar Libya shi ne kawai hanyar kawo karshen rikicin da kasar atke fama da shi tun bayan kisan gillar da suka yi wa tsohon jagoran kasar a lokacin da suka kaddamar da hari da sunan taimaka ma ‘yan tawaye wadanda daga bisani kuma suka gagare su.
Gwamnatocin kasashen lebanon da Libya sun cimma matasa dangane da makomar Imam Musa Sadr da abokan tafiyarsa biyu ta hanyar kafa wani kwamiti da zai bi kadun wannan batu da ya hada dukaknin bangarorin biyu.
Sai kuma wani labarin da ya danganci kasar ta Lebanon da ke cewa, babban Magatarda na Majalisar Doinkin Duniya Ban Ki-moon ya soma wata ziyarar aiki ta tsawon kwanaki uku a kasar Labanan daga yau juma'a, domin tattauna batutuwan da suka shafi rikicin siyasar kasar Syria, da matsayin kotun da kasashen duniya suka kafa domin binciken kisan da aka yi tsohon Firayi ministan kasar ta Labanan Rafikul Hariri da kuma neman gwamnatin Labanan ta karbe illahirin makamai da kungiyar Hizbullah ta mallaka.
A tsawon wadannan kwanaki uku dai, Ban Ki-Moon zai gana da shugaban kasar ta Labanan Mishel Suleman, da Firaministan kasar Najib Mikati, da kuma shugaban Majalisar dokokin kasar Nahbih Beri wanda babban abokin kawance ne ga kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hizbullah, yayin da a gobe asabar zai gana da manyan kwadojin rundunar wanzar da tsaro ta MDD da ke kasar.
To sai dai tun kafin Ban Ki-moon ya isa a kasar, tuni kungiyar Hizbullah ta bayyana ziyarar da cewa al'ummar kasar Labanan musamman ma ma'abota 'yanci ba sa marhabin da ita.
1016759


captcha