Bangaren kasa da kasa: kungiyoyin bayar da agaji na musulunci a kasar Pakistan sun kaddamar da wani shiri mai muhimmancin gaske ga wasu yan gidan yari inda karkashin wannan shiri suna koyar da wasu yan gidan yarin karatun kur'ani mai tsarki da kuma suna zabar wasu daga cikinsu da suke ganin nan gaba idan suka kammala zaman gidan yarin za su taimakawa al'umma a rayuwar zaman takewa da sauran bangarori na rayuwa musamman bangaren ilimi da yada addinin musulunci.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: kungiyoyin bayar da agaji na musulunci a kasar Pakistan sun kaddamar da wani shiri mai muhimmancin gaske ga wasu yan gidan yari inda karkashin wannan shiri suna koyar da wasu yan gidan yarin karatun kur'ani mai tsarki da kuma suna zabar wasu daga cikinsu da suke ganin nan gaba idan suka kammala zaman gidan yarin za su taimakawa al'umma a rayuwar zaman takewa da sauran bangarori na rayuwa musamman bangaren ilimi da yada addinin musulunci.An nakalto daga majiyar labarai ta ON Islam cewa; Muhammad Yunus shugaban komitin wannan shiri ya bayyana cewa: Ta hanyar wannan shiri muna son wankewa mutane masu mummunan tunani da kollon gidan yari kawai guri ne na tsare wadanda suka aikata mummunan aiki kwakwalluwa su san da cewa bah aka ba ne a wannan guri akwai wadanda za su amfani al'umma a nan gaba da ciyar da al'umma inda al'umma za su amfana das u suma su amfana da al'umma kamar sauran mutane saboda haka muka bullo da wannan shiri.A Matakin farko mutane ashirin ne daga cikin yan gidan yarin aka fara koyar das u kur'ani mai girma kuma an samu nasara dab a su hutu na watanni uku kuma a ka ci nasara kan hanakan . A kasashe da daman a duniya ana yi way an gidan yari mummunan kallo alhali lamarin ba haka ne ba.
1018553