IQNA

Makaranta Su Kirkiro Na Salo Ya Fi A Kan Yi Kwaikwayon Wasu makarantan

16:30 - May 29, 2012
Lambar Labari: 2337157
Bangaren kasa da kasa, makaranta kur’ani mai tsarki su kirkiro na salo na karatu ya fi muhimmanci a kan kwaikwayon wasu makarantan na daban domin kuwa hakan ne zai bayar da damar kara yawan salo na karatu a duniyar musulmi da sabunta salo.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a zantawar da ta hada shi da makarancin kur’ani mai tsarki dan asalin kasar Masar mazaunin kasar Birtaniya Muhammad Ayyub Asif, ya bayayna cewa makaranta kur’ani mai tsarki su kirkiro na salo na karatu ya fi muhimmanci a kan kwaikwayon wasu makarantan na daban domin kuwa hakan ne zai bayar da damar kara yawan salo na karatu a duniyar musulmi da sabunta salo daban-daban.
Ya ci gaba da cewa a lokain da mai karatun kur’ani yake kwaikwayon wani maranci a cikin kira’arsa hakan ya kan rage tasirinta koda kuwa yana yin kwaikwayon daidai, ko ma da yafi wanda ake kwaikwayon iya wannan salon, amma inda ba nashi ba ne to tasirin hakan ragagge ne.
Makarancin ya kara da cewa kirkirar salo yana karawa makaranci tabbaci da kansa da kuma salonsa, a lokaci guda kuma yan abarin tarisi a cikin zukatan masu sauraren karatunsa, saboda haka ya yi kira ga dukkanin makaranta da su mayar da hankali wajen kirkiro nasu salon domin amfanar da ‘yan baya da kuma bunkasa karatun kur’ani mai tsarkia duniya.
Muhammad Ayyub ya ce makaranta kur’ani mai tsarki su kirkiro na salo na karatu ya fi muhimmanci a kan kwaikwayon wasu makarantan na daban domin kuwa hakan ne zai bayar da damar kara yawan salo na karatu a duniyar musulmi da sabunta shi.
1012189


captcha