Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Muhammad Bakir Khorramshad ya bayyana cewa tattaunawa tsakanin addinai na duniya da kuma bude zuciya daga dukkanin bangarori na da babban tasiri wajen kara samar da fahimtar juna da zaman lafiya tsakanin dukaknin addinai na duniya wanda kuma ko shakka babu, shi ne bababn ake bukata ahalin yanzu.
Jaridar ta kawo babban labarinta da ke cewa, a jiya ne sabuwar majalisar shawar musulunci ta Iran ta gudanar da zamanta na farko tare da halartar shugaba Ahamdinejad.
Jaridar ta ce an bude taron ne tare da karanta jawabin jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, wanda shugaban ofishinsa da ke birnin Tehran sheikh Muhammad Golpaigani ya karanta.
A cikin bayanin Sayyid Khamenei ya taya dukkanin mambobin majalisar murnar fara aiki, tare da kara tunatar da su irin babban nauyin da ke kan wuyansu, domin gudanar da aikin da jama’a suka zabe su dominsa.
Jagoran ya kara da cewa imani da Allah da dogaro da shi da kuma himma da kwazo da ‘yancin siyasa, shi ne babban siriin na dukaknin ci gaban da kasar ta samu a cikin shekaru 33 da suka gabata na juyin juya halin musulunci. 1019478