IQNA

Za A Yanke Hukunci Na Karshe Kan Husni Mubarak Kna Kisan Jama’a

15:26 - June 02, 2012
Lambar Labari: 2339379
Bangaren kasa da kasa, a gobe ne za a gudanar da zaman shari’a a kotu kan kisan jama’a da ake zargin tsohon shugaban kasar Masar Husni Mubarak da aikatawa a lokacin mulkinsa musamman a lokacin da mutanen kasar suke jerin gwanon hambarar da shi daga kan mulki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, a gobe ne za a gudanar da zaman shari’a a kotu kan kisan jama’a da ake zargin tsohon shugaban kasar Masar Husni Mubarak da aikatawa a lokacin mulkinsa musamman a lokacin da mutanen kasar suke jerin gwanon hambarar da shi daga kan mulki shekarar ta gabata.
A wani labarin kuma karon farko za a fitar da jaridar mabiya mazhabar iyalan gidan manzon allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa tsarkaka mai sunasautin Alilbait wanda cibiyar muslunci ta Algadir za ta dauki nauyin bugawa wadda kuma za ta fara fito nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.
Bayanin ya ci gaba da cewa jagoran jam’iyyar Gadir ta kasar Masar kumababban sakataren majalisar koli ta mabiya tafarkin iyalan gidan manzon allah a kasar masar Muhammad Duraini shi ne ya bijiro da batun bude wannan jaridar, kuma zai bayar da gagarumar gudunmawarsa domin ci gabanta.
Wannan dai shi ne karon farko da za a fitar da wata jarida ta mabiya mazhabar iyalan gidan manzon allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa tsarkaka mai sunasautin Alilbait wanda cibiyar muslunci ta Algadir za ta dauki nauyin bugawa a kasar ta Masar. 1021526

captcha