Bangaren siyasa da zamantakewa, karamin ofishin jakadancin jamhuriyar muslunci ta Iran a birnin Adis ababa na kasar Habasha ya dauki nauyin shirya zaman taro na yin nazari da bahasi kan mahangar Imam Khomeini (RA) dangane da lamurra da dama na addini da kuma fadakar musulmi a duniya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, a ci gaba da tunawa da muassin jamhuriyar muslunci ta Iran karamin ofishin jakadancin jamhuriyar muslunci ta Iran a birnin Adis ababa na kasar Habasha ya dauki nauyin shirya zaman taro na yin nazari da bahasi kan mahangar Imam Khomeini (RA) dangane da lamurra da dama na addini da kuma fadakar musulmi a duniya, kamar yadda muke gani a halin yanzu a kasashen larabawa.
kafofin yada labarai na kasashen yammacin turai suna taka gagarumar rawa wajen karfafa gwiwar masu akidar cin zarafin musulmi da kuma keta alfarmar musulmi da addinin musulunci a duniya kamar dai yadda muke gani a duniya musamman ma a cikin nahiyar turai.
an watsa labarai masu karo da juna dangane da makomar majalisar ministocin kasar masar karkashin jagorancin fira minitsna Kamal Janzuri wanda masu tsaurin ra’yin kishin islama suke tuhumarsa da kasawa yayin da majalisar sojin kasar ba ta ba shi goyon bayn da yake bukata wajen gudanar da ayyukansa na tafiyar da mulki.
Mambobin majasar dokokin kasar Masar sun yi kira da a safke babban malamin kasar mai bayar da fatawa bayan ya yi tafiya zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila ba tare da izinin majalisa da kuma yin shawara da majalisar malaman addinin muslunci ta kasar ba lamarin da ake kallonsa a matsayin wani babban kure.
1022361