IQNA

An Yanke Hukuncin Daurin Rai Da Rai Kan Tsohon Shugaban Kasar Masar Husni Mubarak

17:38 - June 04, 2012
Lambar Labari: 2339906
Bangaren kasa da kasa, kotun hukunta manyan laifuka ta kasar Masar ta yanke hukuncin daurin rai da rai a kan tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Husni Mubarak bayan samunsa da laifin bayar da umurnin kashe fararen hular kasar da suka yi boren da ya kawo karshen mulkinsa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo bna Aljazeera cewa, a jiya kotun hukunta manyan laifuka ta kasar Masar ta yanke hukuncin daurin rai da rai a kan tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Husni Mubarak bayan samunsa da laifin bayar da umurnin kashe fararen hular kasar da suka yi boren da ya kawo karshen mulkinsa a cikin shekarar da ta gabata.
Mambobin majasar dokokin kasar Masar sun yi kira da a safke babban malamin kasar mai bayar da fatawa bayan ya yi tafiya zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila ba tare da izinin majalisa da kuma yin shawara da majalisar malaman addinin muslunci ta kasar ba lamarin da ake kallonsa a matsayin wani babban kure.
Tafiyar da Ali Juma’a ya yi zuwa birnin Qods ya yi ne tare da hadin gwiwa da ma’aikatar tsaro ta haramatcciyar kasar Isra’ila wanda kuma ko shakka babu hakan ya sanya gagarumin shakku a cikin zukatan mutanen kasar dangane da wannan ziyara tasa, duk kuwa da cewa daga cikin abubuwan da ya yi har da duba lafiyarsa a asibiti.
Yan majasar dokokin kasar Masar sun yi kira da a safke babban malamin kasar mai bayar da fatawa bayan ya yi tafiya zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila ba tare da izinin majalisa da kuma yin shawara da majalisar malaman addinin muslunci ta kasar ba duk kuwa da cewa bisa doka sai sun amince masa.
1022234


captcha