Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na chronicle cewa, a karon farko za a bude wata bababr cibiyar yin nazari kan ilmomin kur’ani mai tsarki a kasar Amurka wadda mabiya addinin muslunci na kasar za su dauki nauyin budewa da kuma kula da ita a cikin ‘yan watanni masu zuwa.
A wani labarin kuma shugaban hukumar makamashi ta duniya AIEA, Yukiya da ya kawo wata ziyarar aiki a kasar ta Iran makonni biyu da suka gabata ya ce a ranar juma'a mai zuwa za a yi wata tattamnawar a Vienne tsakanin mataimakin shugaban hukumar Hermann Nakartes, da wakilin kasar Iran a hukumar ta AIEA, Ali As-qar Soltanieh.
Komitin wakilai na hukumar yayi nazarin rahoton Yukiya Amano, dake matsayin cikakken rahoto kan ziyarar aikin da ya kai a cibiyoyi da santoci na sarrafa nukiliya a kasar Iran. Wannan rahoto na cikin wani kundi dake nuna zaman lafiyar shirin nukiliyar kasar ta Iran da cikakken sa idon hukumar game da aiki. Sabon zaman tattamnawar da za a yi nan gaba tsakanin Iran da hukumar ta AIEA zai maida hankali ne kan ayukan na gadangadan game da shirin, a kan abubuwa da suka rage wanda ba su da daurin kai a lamarin koma har su iya kawo cikas wajen cimma yarjejeniya ta karshe. Ala kulli hali dai ana ga sakamakon wannan tatamnawar zai share hanya ga zaman da za a yi tsakanin kasar ta Iran da kasashe 5 da 1 wato kasar Rasha, Chine, Amurka, Birtaniya, da Faransa, hade da Jamus nan gaba.
Bayan watanni 15 na tsaiko, zaman tattamnawar tsakanin kasar ta Iran da kuma wadannan kasashe an koma tattamnawar, a ranar 14 ga watan Afrilu da ta gabata a birnin Istambul na kasar Turkiya, wanda bangarorin biyu suka nuna da cewar zaman ya gudana cikin kyakyawan yanayi, bayan zaman na farko an yi wani na biyu a ranar 23 ga watan jiya a birnin Bagdad na Iraki, wanda shima aka yaba da shi, sai kuma a nan da kasa da sati biyu masu zuwa za a sake zama a birnin Moscou na Rasha. A kan wannan manufa dai, nau'in shawawarin da aka gabatar yau da shekaru 3 daga bangarorin biyu an musu binciken kwakwaf an tattamna a kansu da kyakyawar manufa, kuma a zaman Bagdad an yi bitarsu daya bayan daya don su zamanto gimshikin tattamnawar da za a dogara a kansu daga kowane bangare.
1025819