IQNA

Malazia Za Ta Dauki Bakuncin Taron Harkokin Tattalin Arziki Na Ksashen Musulmi

17:07 - June 11, 2012
Lambar Labari: 2344465
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Malazia za ta dauki nauyin bakuncin zaman taro kan harkokin tattalin arzikin kasashen musulmi wanda zai gudana a karo na takwas a birnin Jauhar na kasar tare da halartar manyan jami’a daga kasashen musulmi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bernama cewa, gwamnatin kasar Malazia za ta dauki nauyin bakuncin zaman taro kan harkokin tattalin arzikin kasashen musulmi wanda zai gudana a karo na takwas a birnin Jauhar na kasar tare da halartar manyan jami’a daga kasashen musulmi da suke taga gagagrumar rawa wajen hababka tattalin arzikin musulmi.
A kasar Pakistan kuwa yanzu haka an fara yin rijistar sunayen mutanen da suke bukatar gudanar da aikin hajjin bana birnin Lahour na kasar wanda shirin yakegudana a halin yanzu babban husainiyar Minhaj da ke birnin kuma kofa bude take har yanzu mutanen da suke bukata tafiya ta wannan hanya a wannan shekara.
Kasar pakistan dai na daga cikin kasashen musulmi da suka fi yawan mabiya wanna addini, inda adadinsu ya kai sama da miliyan dari da saba’in, kuma suna samun gagarumin ci gaba da fuskar yada manufofi na addini ta hanyoyi da suka dace a zamannce kamar yadda ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar ta sanar, wanda hakan ke tabbatar da ci gaban addini a yankin na kudancin nahiyar Asia.
fara yin rijistar sunayen mutanen da suke bukatar gudanar da aikin hajjin bana birnin Lahour na kasar Pakistan wanda shirin yakegudana a halin yanzu babban husainiyar Minhaj da ke birnin kuma kofa bude take har yanzu mutanen da suke bukata, hakan na da matukar muhimmanci wajen samar da hanyoyi mafi sauki ga mutane da suke da niyar gudanar da aikin haji.
1026027


captcha