Bangaren siyasa, abubuwa da dama da suke faruwa a yankin gabas ta tsakiya za su amfanar da al’ummomin palastinu marassa kariya da suke fusknatar babban zalunci daga hramtacciyar kasar Isra’ila ba tare da kasashen duniya masu rajin kare ‘yan adam sun ce uffan a kan hakan.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, abubuwa da dama da suke faruwa a yankin gabas ta tsakiya za su amfanar da al’ummomin palastinu marassa kariya da suke fusknatar babban zalunci daga hramtacciyar kasar Isra’ila ba tare da kasashen duniya masu rajin kare ‘yan adam sun ce uffan a kan hakan ba domin lamarin ya shafi yahudawan sahyuniya.
A kalla 'yan kungiyar al'ka'ida 26 ne aka kashe a kasar Yamen a yau litinin.
Rahotannin da su ke fitowa daga kasar ta Yamen sun ce sojojin gwamnatin Yamen sun kashe 'yan kungiyar ta al'ka'ida 26 a wani hari da ta kai musu a garin Ja'ar da ke kudancin kasar, bugu da kari sojojin na kasar Yamen sun sanar da gano wani rumbun makamai na al'aida a yankin.
Tun a ranar 12 ga watan mayu ne dai sojojin na Yamen su ka fara kai farmaki akan sansanin kungiyar al'ka'ida da ke kudancin kasar, kungiyar agaji ta red Cross ta sanar da cewa mazauna yankin suna da bukatuwa da kayan abinci da magani sai dai babu damar isar da su saboda yawan tashe-tashen hankula.
1027322