Bangaren kur’ani, an sanar da sunayen wasu daga cikin alkalan gasar karatu da hardar kur’ani ta duniya da za a gudanar a jamhuriyar muslunci ta Iran a karo na ashirin da tara dukkanin sunayen da aka sanar dai ya zuwa yanzu na mutane goma 14 iraniyawa ne kamar yadda daga bisani kuma za a san sunayen alkalai daga kasashen ketare.
Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alkalan gasar kur’ani ta kasa cewa an sanar da sunayen wasu daga cikin alkalan gasar karatu da hardar kur’ani ta duniya da za a gudanar a jamhuriyar muslunci ta Iran a karo na ashirin da tara dukkanin sunayen da aka sanar dai ya zuwa yanzu na mutane goma 14 iraniyawa ne kamar yadda daga bisani kuma za a san sunayen alkalai daga kasashen ketare da za su kasance cikin gasar.
An bude wani ofishin kula da harkokin addini na kasar Kyrgystan a kasar Kuwait da nufin kara bunkasa harkokin addini da kuma kyakyawar alaka tsakanin kasashen ta fuskkar bunksa harkokin addini da ilim ga mi da al’adu a tsakaninsu kasantuwarsu mambobi a cikin kungiyar kasashen musulmi.
A cikin wanmnan makon ne wani mutum da ake kira mai bayar da fatawa na gwamnatin Saudiyya Abdulaziz Bin Abdullah Al-sheikh, ya fitar da wata fatawa daga mahangarsa ta akidar wahabiyanci da ke kafirta musulmi kansu wadanda ba su bin wannan tafarki na wahabiyanci, inda ya halasta kaddamar da kai hare-hare kan wuraren ibadar mabiya addinin kirista.
Masana da dama suka ganin a lokacin malaman addinin muslunci na hakika suke ci gaba da hankoron ganin an samu fahimtar juna tsakanin dukaknin al’ummomin duniya tare da zaman lafiya wasu daga cikin masu kiran kansu malaman addini a kasar Sudiyya suna fitar da fatawoyin halascin kai hari kan saura mutane
1028189