Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, sawwaka tafsirin kur’ani mai tsarki na taimaka wa yara masu harda bisa la’akari da cewa a duk lokacin da bayani ya zama mai sauki kuma takaitacce ya fi saurin zama cikin kwalwa kamar yadda hakan ya kan sanya masu hardar sauri wajen kaiwa ga mataki na gaba a cikin hardar tasu.
A zanatawar da ta hada shi da kamfanin dilalncin labaran iqna, Ramin Mehmanparast kakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran ya bayyana cewa samun cikakkiyar hulda tsakanin marubuta na kasashen musulmi hakan zai taimaka matuka wajen fitar muhimman lamurra da musulmi suke yin rubutu a knsu na addini domin amfanin sauran mutanen duniya, musulmi da ma wadanda ba musulmi ba.
Ya ce a koda yaushe marubuta suna taka gagarumar rawa wajen fitar da kowane irin lamari ga sauran mutane, inda sukan yi amfani da hikimar da Allah ya basu wajen ganin sun isar da sako cikin sauki zuwa ga kwakwalwar mai karatu, wanda kuma idan marubuta daga cikin marubutan musulmi suka samu wata kyakyawar dangantaka ko shakka babu hakan zai ba su damar isa da sakon addini da munufofinsa ga sauran al’ummomi.
Mehman paranst kakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran ya bayyana cewa samun cikakkiyar hulda tsakanin marubuta na kasashen musulmi hakan zai taimaka matuka wajen fitar muhimman lamurra da musulmi suke yin rubutu a knsu na addini domin amfanin sauran mutane na duniya baki daya.
1027773