IQNA

Shugabannin Jami’oin Kasashen Musulmi Sun Fara Gudanar Da Zamansu

18:04 - June 13, 2012
Lambar Labari: 2346258
Bangaren kasa da kasa, shugabannin jami’oi na kasashen musulmi sun fara gudanar da zamansu a birnin Islam-abad na kasar pakistan da nufin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci yanayin karatuka akasashen musulmi da kuma sanin hanyoyin da za a bi wajen kara habbaka su.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ISESCO cewa, shugabannin jami’oi na kasashen musulmi sun fara gudanar da zamansu a birnin Islam-abad na kasar pakistan da nufin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci yanayin karatuka akasashen musulmi da kuma sanin hanyoyin da za a bi wajen kara habbaka su kamar yadda ya kama.
Wakilin malaman mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kasar Kuwait Ayatollah Muhammad Baqir Almihri ya kirayi malamin wahabiyawan Saudiyya zuwa ga mneman uzuri ga dukaknin musulmin duniya kan cin zarafin da ya yi wa manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iayalan gidansa tsarkaka, tare da jingina karya ga wannan manzon mai tsarki.
Mutumin wanda ake kira malami a kasar Saudiyya wanda ya shahara da yin izgili da addinin muslunci da manzon Allah da iyalan gidansa tsaraka mai suna Uraifi, ya raya cewa gjiya ba najasa ba ce, domin kuwa a karyarsa kafin haramta giya wasu daga cikin sahabbai suna baiwa manzon Allah giya kyauta, shi kuma yana zubar da ita ko kuma shi ma ya baiwa wasu kyauta.
Wannan cin zarafi ga addini ne ya sanya wakilin malaman mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kasar Kuwait Ayatollah Muhammad Baqir Almihri ya kirayi wannan mutum bahawabiyan Saudiyya zuwa ga mneman uzuri ga dukaknin musulmin duniya kan cin zarafin da ya yi wa manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iayalan gidansa tsarkaka

1028335


captcha