IQNA

Makaman Hizbullah Suna Da Matsayi Na Musamman Domin Kare Lebanon Da Harin Yahudawa

18:03 - June 13, 2012
Lambar Labari: 2346259
Bangaren kasa da kasa, pira ministan kasar Lebanon ya bayyana cewa makaman da kungiyar hizbullah ta kasar take mallaka suna da matsayi na musamman domin kuwa ana kare kasar ne daga duk wata barazana da take fuskanta daga haramtacciyar kasar Isra’ila.
Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadawa na yanar gizo na jaridar Al-intiqad cewa, Najib Mikati pira ministan kasar Lebanon ya bayyana cewa makaman da kungiyar hizbullah ta kasar take mallaka suna da matsayi na musamman domin kuwa ana kare kasar ne daga duk wata barazana da take fuskanta daga haramtacciyar kasar yahudawan sahyuniya.
Sai kuma wani labarin da ke cewa jagororin mabiyan addinan kiristanci da muslunci a yankin Jubail na kasar Lebaon sun gana a babban ginin majami’ar Sin Jan da ke yankin dangane muhimman batutuwa da suka danganci bangarorin biyu da za su taimaka wajen kara samun fahimtar juna a tsakaninsu.
Taron tsakanin bangarorin biyu ya gamsar da masu halatarsa, bisa la’akari da irin yadda kasar Lebanon ta zama wurin buga misali na fahimtar juna tsakanin mabiya addinan kirsitanci da muslunci, duk kuwa da yakin basasa da bangarorin biyu suka yi a lokutan baya wanda aka jaza musu da nufin wargaza su, amma kuma hakan sai ya zama wani dalili na hada kansu.
Manyan jagororin mabiyan addinan kiristanci da muslunci a yankin Jubail na kasar Lebaon sun gana a babban ginin majami’ar Sin Jan da ke yankin dangane muhimman batutuwa da suka danganci bangarorin biyu da za su taimaka wajen kara samun fahimtar juna mai dorewa.
1028145


captcha