IQNA

Bugawa Tare Da Yada Wani Littafi Da Ke Bayani kan hakikanin Musulunci A Nahiyar Turai

18:39 - June 15, 2012
Lambar Labari: 2347108
Bangaren kasa da kasa, an buga tare da yada wani littafi mai magana kan hakikanin musulunci da mahangars a akan dukkanin lamurra na rayuwa da sauran addinai da kuma yadda yake kira zuwa ga zaman lafiya a tsakanin dukaknin al’ummomin duniya baki daya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na ISESCO cewa, an buga tare da yada wani littafi mai magana kan hakikanin musulunci da mahangars a akan dukkanin lamurra na rayuwa da sauran addinai da kuma yadda yake kira zuwa ga zaman lafiya a tsakanin dukaknin al’ummomin duniya baki daya manufar hakan kuwa ita ce, kara fito da matsayin addinin muslunci da manufofinsa, sabanin abin da ake kirkira na karya a kansa da mabiyansa a cikin kasaseh yammacin turai.
Wani labarin kuma ya ce limamin juma'a a nan birnin Tehran, ya ce kisan da makiya ke yi wa malaman kimiya na kasar, ba abin da zai cusa wa al'ummar kasar face farkawa da kuma kare martabobin kasar a kowadanne fagage na rayuwa, musamman wannan bangare na ilimimin nukiliya da Iran take ggudanar da ayyukanta a cikin na zaman lafiya domin amfanin fararen hula.
A lokacin da yake gabatar da hudubar sallar juma'a a masallacin jami'ar Tehran a yau, Ayatullahi Mohammad Emami-Kashani, ya ce kisan na baya-bayan nan da makiya suka yi wa malamin kimiyyar nukiliya na kasar mai suna Mustafa Ahmadi Roshan, wata alama ce da ke kara nuna wa duniya irin damuwar da kasashe da ke hamayya da Iran din ke da ita dangane da irin ci gaba da kuma 'yancin da kasar take da shi na dogoro da kai a fannoni na bincike da kuma kimiya.
1029034


captcha