Bangaren siyasa da zamantakewa, wani fitaccen malamin jami’a a kasar Thailand professor Keit Lort Poiton ya bayyana cewa gagarumin ci gaban da jamhuriyar musulunci ta Iran ta samu hakan ya zo ne bayan samun nasarar juyin juya halin musulunci a kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, wani fitaccen malamin jami’a a kasar Thailand professor Keit Lort Poiton ya bayyana cewa gagarumin ci gaban da jamhuriyar musulunci ta Iran ta samu hakan ya zo ne bayan samun nasarar juyin juya halin musulunci a kasar wadda akasarin mazaunat ba mabiya addinin muslunci ba ne.
Malamin ya bayyana hakan a wagaban wani babban taro da aka kira na tunawa da ranar shahadar Imam bakir Sadr a birnin Najaf mai alfarma, wanda ya samu halartar masana daga sassa daban-daban na duniyar musulmi da ma kasashen Asia da dama, gami da manyan malaman addini da na jami’oi na kasar Iraki, inda ya bayyana siffofinsa da cewa mutum ne da ya sadaukantar da ransa saboda Allah da kuma daukakar addinin Allah.
malamin addinin musluncin nan na kasar Tunisia Tijani Samawi ya bayyana cewa Imam Shahid Bakir Sadr baya ga cewa shi ne mutum na farko a cikin larabawa da ya fara fitar da tunain mikewar al’ummar larabawa domin kalubalantar azzaluman shugabanninsu, shi ne kuma mutumin da ya kalubaanci zalunci dawagitan Iraki ba tare da wani shayi ba.
1031800