Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, professor Khan Martos wani malami a jami’ar Compol da ke birnin Madrid ya bayyana cewa fadakar da aka fara samu a cikin kasashen larabawa ta fara game sauran kasashe musamman ma dai na mabiya addinin muslunci daga cikinsu inda suke fara neman hakkokinsu na siyasa da aka haramta musu.
An ware wasu makudan kudade da suka kai dalar Amurka miliyan saba’in domin gudanar da ayyuak na musamman da suka shafi muslunci a kasar Malzia a cikin kasafin kudi na wannan shekara da nufin bunkasa harkokin addinin muslunci a fadin kasar, wadda take daya daga cikin kasashen musulmi.
A wani baynin kuma an gudanar da taron baje klin kur’ani a India, a wajen taron na bajen kolin an nuna kwafi-kwafi na kur’ani mai tsarki wadanda aka rubuta da hannu a kasashen musulmi daban-daban, haka nan kuma wadanda aka buga su a kasashen musulmi, da nufin kara fito da matsayin wannan littafi mai tsarki, tare da bayyanawa duniya cewa matsayinsa yana damfare ne da rayuwar mabiya addinin muslunci, domin ya zama hannunka mai sanda ga masu keta alfarmarsa.
Gudanar da taron baje koli na kasa da ake yi a kasar Pakistan inda ake nuna wasu daga cikin manyan kwafin kur’ani mai tsarki a ginin babbar cibiyar yada al’adun muslunci da ke birnin Lahor na kasar, na dag acikin muhimamn ayyuka da gwamnatin kasar pakistan ke aiwatarwa akowace shekara. Amma a wannan shekara lamarin ya dauki sabon salo na kara kawata taron.
1031885