IQNA

Yin Nazari Kan Matsalolin Da Masu Isar da Sakon Musulunci Ke Fuskanta

21:09 - June 19, 2012
Lambar Labari: 2350126
Bangaren siyasa da zamantakewa, an gudanar dawani zaman taro domin yin nazari kan matsalolin da masu isar da sakon addinin muslunci suke fuskanta a kasar Tanzania tare da halartar masana da malaman addini da kuma wakilan cibiyoyin naddini na kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Alalam da ke watsa shirinsa kan tauroron dan adam daga birnin Tehran cewa an gudanar dawani zaman taro domin yin nazari kan matsalolin da masu isar da sakon addinin muslunci suke fuskanta a kasar Tanzania tare da halartar masana da malaman addini da kuma wakilan cibiyoyin naddini na kasar wadda day ace dag acikin kasashen Afirka masu yawan musulmi.
A halin yanzu rayuwar muslunci ta fara dawowa atsakanin al’ummar kasar Tunisia ta fuskokin zamantakewa da siyasa kamar yadda za a iya sheda hakan daga yanayin dabiu da halayen jama’a tun bayan samun nasarar juyin juya halin da ya kai ga kawo karshen tsohuwar gwamnati ta tsohon shugaban mulki kama karya na kasar.
A wani labarin kuma gwamnatin kasar Tunisiya ta kara waadin dokar-ta-baci da ake aiki da ita a kasar zuwa karshen wannan wata na Apirilu, kamar yanda wata sanarwar da aka fitar a daren jiya take bayyanawa, kakakin shugaban kasa ya bayyana cewa shugaba Moncef Marzouki ya ba da izinin kara wata guda ne na aiki da dokar-ta-bacin bayan da ya yi shawarwari da shugaban majalisar girka kundin tsarin mulki Mustapha Ben Jaafar da kuma Piraminista Hamadi Jebali.
Sanarwar gwamnatin ta ce dalilan da suka sa aka kara waadin wannan doka su ne barazana iri iri da zasu iya janyo tashe tashen hankali a kasar, wani shaharren dan jarida mai sharhin siyasa na kasar Tunisiya Salahuddin Jorchi ya ce da ma can ana tsammanin gwamnati zata dauki wannan mataki domin har yanzu akwai zaman dar dar a tsakanin alumma duk da cewa an sami kyautatuwar yanayin tsaro.
1032202
captcha