Bangaren kas ada kasa, yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra’yi sun kai farmaki kan palastinawa fararen hula mazauna yankunan gabar yamma da kogin Jordan tare da takura musu da cin zarafinsu da ma korarsu daga cikin yankunansu ba tare da kasashen turai sun ce uffan kan hakan ba.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya naklato daga tashar talabijin ta Press TV cewa, yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra’yi sun kai farmaki kan palastinawa fararen hula mazauna yankunan gabar yamma da kogin Jordan tare da takura musu da cin zarafinsu da ma korarsu daga cikin yankunansu ba tare da kasashen turai sun ce uffan kan hakan ba, bil hasali ma suna samun goyon baya da karfafa gwiiwa daga wadannan kasashen na yamamacin turai kan wannnan ta’addanci.
dadin palastinawan da suka yi shahada a yankin zirin Gaza a cikin kwanaki ya karu zuwa 9 sakamakon hare-haren ta'addancin da jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila suke kai wa kan palastinawa fararen hula da ke yankin, rahotanni sun tabbatar da cewa hare-haren na yau sun yi sanadiyar shahadar wani matashi bapalastine a yankin Hayyi Zaitun, jim kadan bayan wani harin da sojojin yahudawan Isra'ila suka kai kan wani gida a yankin, wanda ya yi sanadiyar rasuwar wata karamar yarinya dab a ta wuce shekara daya da haihuwa ba.
A nasu bangaren dakarun gwagwarmaya sun mayar da martani ta hanyar harba makaman roka a kan yankunan da haramtacciyar kasar Isra'ila ta mamye, tun kimanin kwanaki uku da suka gabata ne haramtacciyar kasar Isra'ila ta fara kaddamar da hare-hare kan fararen hula ayankin Gaza da sunan yunkurin murkushe palastinawa 'yan gwagawarmaya, lamarin da ya yi sanadiyar shahadar palastinawa 9 tare da jikkatar wasu daruruwa.
1033349