Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar tlabijin din Al-manr cewa yin kisan gilla a kan mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da kasashen larabawa musamman ma Saudiyya suke yi tare da taimakon Amurka da yahudawan sahyuniya wani babban makirci ne domin haddasa rikici tsakanin mabiya addinin muslunci a cikin kasashen yankin gabas ta tsakiya.
Shigar da kara kan mutanen da suke nuna matuar adawa da addinin muslunci a kasar faransa saboda abin da suke yi na kokarin haddasa rikici da rashin fahimtar juna tsakanin mabiya addinin musulunci da sauran mabiya addainai, yin hakan zai zama tamkar wani hannunka mai sanda ga sauran masu irin wannan akida asauran kasashen turai.
Majalisar mabiya addinin muslunci a kasar Faransa za ta shigar da kara kan mutanen da suek nuna matuar adawa da addinin muslunci a kasar faransa saboda abin da suke yi na kokarin haddasa rikici da rashin fahimtar juna tsakanin mabiya addinin musulunci da sauran mabiya addainai da suke zaune a kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa kasar Faransa na daga cikin kasashen nahiyar turai da suka fi yawan musulmi, ta yadda adadinsu ya zama su ne na biyu ta fuskacin yawa a kasar bayan mabiya addinin kiristanci, amma kuma duk da haka har yanzu gwamnatin kasar ba ta amince da addinin musulunci a hkumance ba amatsayin daya daga cikin addinain kasar, duk kuwea da cewa ta amince da addinin yahudanci.
1033468