IQNA

Taro Karawa Juna Sani Kan palastinu Da Kuma Fadakar Musulmi A Birnin Beirut

21:59 - June 21, 2012
Lambar Labari: 2351515
Bangaren kasa da kasa, taro kan palastinu da kuma fadakar musulmi a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon tare da halartar masana daga jami’in kasar wadanda suka gabatar da laccoci da kasidu dangane da irin yanayin da ake ciki a kasashen da aka yi juyi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar cewa taro kan palastinu da kuma fadakar musulmi a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon tare da halartar masana daga jami’in kasar wadanda suka gabatar da laccoci da kasidu dangane da irin yanayin da ake ciki a kasashen da aka yi juyi wanda kuma ga alama kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
Masana da dama suka ganin a lokacin malaman addinin muslunci na hakika suke ci gaba da hankoron ganin an samu fahimtar juna tsakanin dukaknin al’ummomin duniya tare da zaman lafiya wasu daga cikin masu kiran kansu malaman addini a kasar Sudiyya suna fitar da fatawoyin halascin kai hari kan saura mutane da ba musulmi ba, bisa ijma’in Malamai abin da suke yi yayin hannun riga da musulunci.
mabiya addinin muslunci a kasar Amurka sun nuna rashin amincewarsu da matakan da mahukuntan kasar suke dauka a kansu ta hanyar takura musu da tura musu masu aikin leken asiri wanda hakan ya yi hannun riga da dukaknin dokoki na ‘yan kasa amma su musulmi ana mu’amala da su kamar ba ‘yan kasa ba.
a wani bayani da ya gabatar a gidan talabijin din kasar Faransa a zantawar da ta hada shi da gidan talabijin shugaban kasar Nikola Sarkozy ya bayyana cewa ba su lalae marhabin da Yusuf Qardawi bisa zarginsa da tunzura mutane wajen aikata ayyukan ta’addanci da kuma tsatsauran ra’yi, wanda a cewarsa Faransa ba ta amince da hakan ba.
Shugaban kasar ta Faransa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gudanar da wata zantawa tare da sarkin kasar wanda daya ne daga cikin amintattu ga kasar Faransa, kuma shi ne wanda ya ajiye Qardawi a kasar bayan mahukuntan Masar sun kore shi sakamakon matakan da yake dauka na tunzura mutane zuwa tsatsauran ra’ayi, wanda kuma hakan ya kawo rashin jituwa tsakanin da Masar.
1033866


captcha