Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam cewa, tun a daren jiya ne dubban daruruwan mutane na gudanar da zanga-zangar kin amincewa da ci gaba da mulkin da sojoji suke gudanarwa akasar Masar tare da hambarar da majalisar dooki da mutanen kasar suka zaba a cikin watannin da suka gabata lamarin da ya harzuka mutane musamman ma masu kishin islama daga cikinsu ad suke da rinjaye a majalisar.
Dan takaran kungiyar Ikhwan Muslimin a zaben shugaban kasar Masar da aka gudanar Muhammad Morsi ya ja kunne dangane da abin da zai biyo bayan kokari magudi da wasa da kuri'ar da al'ummar kasar suka kada a zaben shugaban kasar da aka gudanar.
Muhammad Morsin ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da manema labarai a yau din nan inda ya ce kungiyar tasa dai ba ta nufin tada rikici ko kuma fuskantar wani amma dai ba za taba amincewa da magudin zabe ba. Har ila yau Muhammad Morsin ya soki lamarin sojoji masu mulkin saboda irin ikon da suka ba wa kansu da kuma rusa majalisar kasar wanda ya ce kungiyar tasa ba za ta amince da hakan ba.
Wannan kalami ya zo ne a daidai lokacin da al'ummar kasar musamman na birnin Alkahira suke ci gaba da taruwa a dandalin Tahrir da ke tsakiyar birnin don nuna rashin amincewarsu da matakan da sojoji masu mulki a kasar suke dauka wanda suke ganinsa a matsayin juyin mulki ga juyin juya halin kasar.
A bangare guda kuma majalisar sojin kasar Masar din ta fitar da wani bayani da ke jan kunnen mutanen kasar da cewa za su dauki tsauraran matakan a kan duk wani da ya yi kokarin wasa da tsaron kasar wanda ake ganin hakan a matsayin ishara ne ga 'yan Ikhwan din da sauransu da suke shirin gudanar da zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaben shugaban kasar matukar dai aka sanar da cewa ba dan takaransu ne ya lashe zaben ba.
Har yanzu dai mahukuntan kasar Masar din ba su sanar da sakamakon zaben ba, lamarin da wasu suke ganinsa a matsayin wani kokari na yin magudin zabe da sanar da tsohon firayi ministan kasar Ahmad Shafiq a matsayin wanda ya lashe zaben.
1035317