IQNA

Makaranta Kur’ani Daga Nahiyar Asia Suna Bin Salon Karatunsu Na Gargajiya Ne

17:10 - June 23, 2012
Lambar Labari: 2352583
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin makarnta kur’ani mai tsarki da ya halarci gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa da aka gudanar a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar musulunci ta Iran ya bayyana cewa akasarin makaranta daga nahiyar Asia suna bin salon karatu na gargajiyar yankunansu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Safar Muraduf daya daga cikin makarnta kur’ani mai tsarki da ya halarci gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa da aka gudanar a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar musulunci ta Iran ya bayyana cewa akasarin makaranta daga nahiyar Asia suna bin salon karatu na gargajiyar yankunansu musamman daga gabacin nahiyar.
Ya ci gaba da cewa gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki wata babbar dama ce ga makaranta da mahardata na kasashen musulmi da su san juna su samu masaniya kan harkokin addini a sauran kasashen duniya musamman ma a bangaren karatun kur’ani mai tsarki a mataki na duniya baki daya.
An nuna wasu daga cikin kwafin kur’ani mai tsarki da aka buga a cikin harsunan duniya daban-daban da suke da alaka da yarukan da ake yin rubutu da su domin isa da ilmomi ga sauran mutane na sassan duniya da nufin kara isar da sakon da ke tatatre a cikin kur’ani mai tsarki.
yanzu haka an fara yin rijistar sunayen mutanen da suke bukatar gudanar da aikin hajjin bana birnin Lahour na kasar Pakistan wanda shirin yakegudana a halin yanzu babban husainiyar Minhaj da ke birnin kuma kofa bude take har yanzu mutanen da suke bukata tafiya ta wannan hanya a wannan shekara.
1035353



captcha