IQNA

Samun Zaman Lafiya A Gabas Ta Tsakiya Na bukatar Kawo Karshen Gwamnatin Sahyuniya

17:07 - June 23, 2012
Lambar Labari: 2352593
Bangaren kasa da kasa, samun zaman lafiya mai dorewa ayankin gabas ta tsakiya na bukatar kawo karshen gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ne baki daya kafin al’ummomin yankin da sauran al’ummomin duniya su samu su sarara daga wannan gwamnati ta ‘yan ta’adda.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Alamanar cewa, Sheiklh Nabil Kwuk ya babbana cewa samun zaman lafiya mai dorewa ayankin gabas ta tsakiya na bukatar kawo karshen gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ne baki daya kafin al’ummomin yankin da sauran al’ummomin duniya su samu su sarara daga wannan gwamnati ta ‘yan ta’adda masu lasisi daga manyan gwamnatocin duniya.
A nasa bangaren babban sakataren kungiyar gwagwarmayar musulunci a kasar Lebanan Sayyid Hassan nasrullah ya jadadda goyon bayansa ga jagoran juyin juya halin muslunci da kuma shugaban jamhuriyar musulunci ta Iran kan gagarumar gudunmawar da suke bayarwa adukaknin bangarori na ci gaba n al’ummar musulmi.
Kasar Iran na gamsuwa da yanda matsayi da karfi da darajar kasar Iraki, ke bunkasa yau da gobe a cikin duniyar larabawa da musulmi, inji jagoran juyin juya halin musulumci na Iran, Ayatullah Ali Khamenei, yayi wannan furuci ne jiya litinin yayin da ya gana da praministan kasar ta Iraki Nuri Almaliki, da ya kawo wata ziyara a nan Teheran. Jagoran ya kara da cewa, kokarin da zai taimaka wajen kara tabbatar da karfin magabatan kasar ta Iraki, musamman game da jihadi na kimiya hade da ayukan sake gina kasar, sune za su habbaka matsayin kasar da cimma guri da bukatun al'ummar kasar da ma gwamnatin kasar baki daya. Inda ya nuna cewar irin abubuwan da suka gudana a cikin kasar a yan watannin nan, sun farkar da gwamnati da al'ummar kasar game da irin matsayi da kuma rawar da za su iya takawa a cikin duniyar larabawa da musulmi.
1035288

captcha